Logo

Catholic Diocese of Katsina

Back to events

ADDU’A, AZUMI DOMIN ZABUBBUKA NA SHEKARAR 2027

11/8/2026

ADDU’A, AZUMI DOMIN ZABUBBUKA NA SHEKARAR 2027

Ya ku ’yan’uwana Limamai, ’yan’uwa maza da mata masu rayuwar tsarkake kai, da ’yan’uwa ƙaunatattun ’ya’yan Allah,

Alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu da salama su kasance tare da ku!

Yayin da ƙasarmu Nijeriya ke shirin gudanar da babban zaɓen ƙasa na shekarar 2027, ina kira ga kowa da mu haɗa kai cikin addu’a da azumi saboda ƙasarmu.

Bisa kiran da Ƙungiyar Taron Bishoshin Katolika ta Nijeriya (CBCN) ta yi, ya kamata mu fahimci cewa sahihancin zaɓe babatun siyasa kawai ba ne, har ma da nauyin ɗabi’a da naruhaniya. Rikicin zaɓe, sayen ƙuri’u, maguɗi, cin hanci da rashawa, da rarrabuwar kawuna bisa ƙabila ko addini, duk suna barazana ga zaman tare da kuma mutuncin ɗan Adam. A matsayimmu na Kiristoci, baikamata mu yi shiru ko zaman kasha wando ba.

A ƙarƙashin taken “Adalci da Salama Su Gudana Kamar Kogi” (Amos 5:24), an kira mu da mu zama masu kawo gaskiya, adalci, salama da sabunta ƙasa. Addu’a dole ta zaburar da mu zuwaga aiki, bangaskiyarmu kuma ta bayyana ta hanyar zama ’yan ƙasa masu kishin ƙasa da riƙon amana. Dole ne mu dage da addu’a, mu ƙi duk wani nau’in maguɗin zaɓe, mu guji tsoratarwa da yaudara, sannan mu ƙarfafa zaman lafiya da shiga tsarin dimokuraɗiyya cikin lumana.

Saboda haka, ina roƙon kowane Farish,  iyalai da kowane mutum a faɗin Diocese ɗinmu da su kiyaye ranakun addu’a da azumi kamar yadda aka tsara:

Asabar, 28 Nuwamba 2026: Ranar Addu’a da Azumi

Talata, 8 Disamba 2026: Ranar Addu’a da Azumi, a ranar Bikin Budurwa Maryamu

Juma’a, 15 Janairu 2027: Ranar  ta Addu’a da Azumi a jajiberin zaɓen Shugaban Ƙasa da na ’Yan Majalisar Tarayya.

A ranakun addu’a da azumiza, a gudanar da azumi, addu’ar Rosary Mai Tsarki, da jerin gwano idan hali yayi, Hadayar Missa, da kuma addu’ar CBCN domin sahihin zaɓe da zaman lafiya a Nijeriya a shekarar 2027.

Ranar Addu’a ta Diocese ta haɗa limamai, masu rayuwar addini, da ’yan’uwanmu masu darikar Katolika domin haɗa kai wajen roƙon Allah.

Waɗanda bazasu iya yin azumi saboda tsufa, rashin lafiya kowasu dalilai, ana ƙarfafasu da su miƙa addu’o’insu da sauran ayyukan sadaukarwa gwargwadon ƙarfinsu.

Ina roƙon fadodinmu da sistoci, Katikis, da shugabanni su jagoranci wannan shirin na ruhaniya da himma, tare da tabbatar da cewa mabiya sun fahimci muhimmancin addu’a da kuma shiga harkokin zaɓe cikin gaskiya da riƙon amana. Bari kowane Farish ya zama cibiyar addu’a, wayar da kanjama’a, sulhu da zaman lafiya.

A matsayimmu na Kiristoci, yakamata mu ƙarfafa ’yan’uwanmu ’yanƙasa da suyi rajistar zaɓe, su mallaki katin zaɓensu na dindindin (PVC), suyi amfani da haƙƙinsu na zaɓe cikin gaskiya da hankali, sannan su kare sahihancin ƙuri’unsu ta hanyoyin da doka ta tanada kuma cikin lumana. Mu ƙi ƙiyayyar ƙabila, rashin haƙuri ga addinin wasu, rikicin siyasa, cin hanci da rashawa, da duk wani nau’in maguɗin zaɓe. Amincinmu ga Almasihu da ƙudurinmu nayiwa al’umma hidima dole su kasance sama da muradun kowace jam’iyyar siyasa.

Ya ku ’yan’uwa maza da mata, Nijeriya tana buƙatar addu’o’inmu, amma tana kuma buƙatar lamirinmu, jarumta da jajircewarmu. Kada mu taɓa yanke ƙauna, ko bari bambance-bambancenmu su rusa haɗin kan ɗan Adam. Mu tuna cewa ƙuri’ar zaɓe kayan aiki ne na ɗaukar nauyi, bana ƙiyayya ba; dama ce ta hidima, ba ta biyan son zuciya ba.

Ta wurin roƙon Budurwa Maryamu Mai Albarka, Sarauniyar Nijeriya, Allah Yaba ƙasarmu shugabanni masu tsayawa kan adalci, kare mutuncin ɗan Adam, tabbatar da zaman lafiya, da yin aiki da gaskiya domin jin daɗin kowa, musamman matalauta da waɗan da ke cikin mawuyacin hali.

Allah yasa addu’o’inmu da ayyukanmu na haɗin kai su taimaka wa Nijeriya wajen gudanar da zaɓe da zai nuna ainihin muradin jama’a, kuma yahaifar da zaman lafiya, haɗin kai da shugabanci nagari.

Adalci ya gudana. Salama ta tabbata. Nijeriya ta bunƙasa!

Ina tare da ku cikin addu’a

Naku cikin Almasihu,

 

+ Gerald Mamman Musa

Bishof na Katsina

Photo Highlights

Event image 1

I want to learn more about _